Mutanen da suka mutu a Sakkwato sun karu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu garkuwa da mutane

Ana ci gaba da samun karin bayani akan yunkurin kubutar da wasu turawa biyu da aka sace a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya wanda bai yi nasara ba.

Ganau sun bayyanawa Wakilin BBC a Sokoton, Haruna Shehu Tangaza, cewa baya ga Christopher McManus, dan Burtaniya, da kuma Franko Lamolinara, dan Italiya, an kashe wasu mutane uku.

Malam Murtala Nabono Tsafe, wanda gidansa ke kusa da inda lamarin ya auku, ya ce ya ga gawar mutane hudu -biyu daga cikinsu farar fata.

Gwamnatin Burtaniya ta ce ita ta shirya yunkurin ceto mutanen tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya.

Firayim Ministan kasar David Cameron ya ce, ''Muna jiran tabbacin karin bayanin da muka samu akan lamarin. Amma dai alamu sun nuna cewa wadanda suka yi garkuwa da su ne suka hallaka su''.

Italiya ba ta da masaniya game da yunkurin ceto

A Italiya jama'a na ci gaba da yin tambayoyi akan abin da ya sa ba a sanar da gwamnatin kasar ba, kafin yunkurin ceto mutanen har sai da aka tura dakaru.

Firayim Ministan kasar, Mario Monti, ya ce ta waya kawai Firayim Ministan Burtaniya ya sanar da shi.

Wani dan Majalisar Dokokin kasar ya bukaci a yi masa bayani akan abin da ya sa ba a shawarce shi ba akan batun.

Karin bayani