Matsalar fari a yammacin Afrika

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar agaji ta OXFAM

Kungiyar agaji ta OXFAM ta ce farin da ake fama da shi a yammacin Afrika, ka iya zama wani bala'i idan ba'a dauki matakan gaggawa ba.

Kungiyar tace kasashen duniya sun yi jinkiri, wajen kai doki a kusurwar Afrika da kuma gabashin Afrika a bara, don haka bai kamata hakan ta sake faruwa ba.

Ta ce yara fiye da miliyan daya na fuskanatar barazanar kamuwa da tamowa .

Wani wakilin BBC da ya ziyarci yankin a baya bayanan yace al'amura sun kara tabbabarewa saboda matsalar yan gudun hijira, sakamakon fada tsakanin soja da masu tada kayar yan kabilar Taureg.