Zaa zaftarema 'yan wasan klub din Rangers albashi

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan wasan Rangers sun amince a zaftare masu albashi domin ceto klub din

BBC ta samu labarin yan wasan Rangers sun amince da a matukar zaftare masu albashi domin ceto klub din daga durkushewa.

Steve Whittaker da Steven Naismith tuni suka cimma matsaya akan a zaftare kashi 75 cikin dari na albashinsu.

Ana ganin cewar sun yanke wanan shawarar ne domin taimakawa shugabannin klub din watau Duff da Phelps domin kada a kori yan wasa da dama a zakarun Scotand.

Shugabannin klub din sun jinkirta har zuwa yau juma'a sanarwar rage guraben aiyukan yi domin cimma matsaya da yan wasan kwallon kafa.

Daya daga cikin shugabannin klub din Paul Clark yace a ranar talatar data gabata yace yana karfin gwiwar cewa zasu cimma matsaya.

Yace hakan zai nuna cewar sunyi dai dai da lokacin da suka dauka wurin aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu.

''Mun shiga matakin karshe na wannan tsari kuma zaa matukar zaftare albashi'' ya shaidawa BBC.

BBC ta samu labarin cewa yan wasan kwallon kafa na klub din da suka shahara an nemi amincewarsu a kan a zaftare masu kashi 75 cikin dari na albashinsu, wadanda ke karban albashi matsakaici su kuma za'a zaftare masu kashi hamsin cikin dari yayinda masu karban albashi mafi kankanci zaa zaftare masu kashi ashirin da biyar cikin dari.