Kotu ta yi watsi da bukatar jami'an Kenya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Uhuru Kenyatta

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ki amincewa da bukatar wasu fitattun 'yan kasar Kenya su hudu ta yin watsi da tuhumar da ake yi musu da ta shafi tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar na 2007.

Ana zargin mutanen ne da suka hada da 'yan takarar shugaban kasa biyu, wato Uhuru Kenyatta da William Ruto da kitsa tashin hankalin, wanda ya yi ajalin sama da mutane dubu daya.

Mista Kenyatta da Mista Ruto dai sun ce babu kanshin gaskiya a zargin.

Mista Kenyatta, wanda shi ne ministan harkokin kudin kasar, ya yi murabus daga mukaminsa bayan da kotun ta fara tuhumarsa.

Karin bayani