An yi zanga-zanga a babban birnin Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Libya

Dubban 'yan kasar Libya ne suka yi wani gangami a Tripoli don yin Allah wadai da yunkurin dattawan yankunan Gabashin kasar na kafa wani yanki mai kwarya-kwaryar 'yanci.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera wakokin hadin kan kasar, suna ta dukan hotunan Abdallah Al Sanusi, shugaban hukumar wucin gadin kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce sun gudanar da ita ne don tabbatar da hadin kan Libya, da yankunanta, da kuma jama'arta:

''Muna kuma tabbatar da cewa a gaba Libya za ta kasance kasa mai adalci ba mai nuna bambanci ba''.

Abdallah Sanusi dai ya ce a shirye ya ke ya tattauna da sauran shugabannin kasar a kan batun.

Karin bayani