An kai harin bam a wata majami'a a Jos

Barnar da wani bam ya yi wanda ya tashi a garin Suleja Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barnar da wani bam ya yi wanda ya tashi a garin Suleja, Najeriya

Rahotanni na cewa wani bam wanda ya tashi a wata majami'a ya hallaka akalla mutum uku a Jos, babban birnin jihar Filato dake arewacin Najeriya.

Al'amarin dai ya auku ne a majami'ar St Finbarr ta mabiya tafarkin Roman Katholika.

Birnin na Jos dai ya jima yana fama da rikicin addini da kabilanci da suka yi sandadiyyar mutuwar mutane da dama cikin shekaru goman da su ka gabata.

Harin bam din a majami'ar katolika dai ya zo makwanni biyu daidai, bayan da wani harin bam na kunar bkin wake a hedikeatar majami'ar COCIN dake birnin na Jos ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane shida da kuma jikkata sama da arba'in.

A baya-bayan nan dai ba jihar Filato kadai ta fuskanci tashin bama-bamai, a a domin kuwa suma wasu jihohin arewacin Nijeriya na fusknatar irin wadandan hare-hare na bama-bamai da kum na bindiga da kn yi snadiyar hasarar rayukan farar hula da kuma jami'an tsaro.

Kawo yanzu dai babu wanda ya duaki alhakin kai harin na yau a maja'mi'ar a Jos, yayin da yanzu haka jama'ar birnin ke kaffa-kaffa da zurga zurga saboda fargabr abinda ka iya biyo baya, sabo da tarihin birnin na yawan tashin hankali.

Karin bayani