Mutane hudu sun mutu a harin da aka kai Nairobi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani mutum da ya jikkata a harin da aka kai Nairobi

Mutane hudu sun mutu sannan wasu da dama suka jikkata bayan wadansu jerin fashe-fashen gurneti a tsakiyar Nairobi, babban birnin Kenya.

Yawancin wadanda suka samu raunukan na cikin mawuyacin hali.

Lamarin ya auku ne a daya daga cikin tashohin mota da suka fi cika a birnin.

Wani kakakin 'yan sanda a Kenya ya ce lamari wani nau'i ne na irin wahalhalun da suke sha a yunkurin su na ganin 'yan uwansu a Somalia sun samu zaman lafiya.

Ko a bara ma an samu lamari mai kamar haka bayan da Kenya ta tura dakarun ta zuwa Somalia don yakar kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab.

Karin bayani