Obama ya koka kan kisan da sojin Amurka ya yi a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama ya yiwa Karzai wayar tarho

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi wa shugaban Afghanistan Hamid Karzai waya don nuna kaduwa da bakin cikin sa akan yadda wani sojan Amurka ya kashe wasu 'yan Afghanistan goma sha shida.

Mista Obama mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'umar Afghanistan sakamakon kisan.

Ya ce zai tabbatar cewa an gano tushen dalilan da suka sanya sojin kasar ya aikata wannan aika-aika, kana a hukunta wanda aka samu da laifi.

Su ma Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Leon Panetta, da jakadan wucin-gadi na Amurka a Afghanistan, James Cunningham, sun ce suna fatan lamarin ba zai sanya dangantakar Amurka da Afghanistan ta yi tsami ba.

Ya kamata gwamnati ta dauki mataki

Dattawa da sauran shugabannin kalibu a Afghanistan sun bukaci Shugaba Hamid Karzai da ya gaggauta daukar matakan gano yadda aka yi sojan Amurka ya iya shiga wani kauye da asubahin ranar Lahadi har ya hallaka mutane sha shida ciki har da yara kanana.

Tuni dai shugaban ya tura wata tawaga zuwa Kandahar, wadda mahaifar sa ce kuma matattar 'yan Taliban.

Wasu mutanen kauyen da lamarin ya faru sun ce watakila ma ba soja daya ba ne ke da hannu a lamarin.

Karin bayani