An gurfanar da Hissen Habre, tsohon shugaban Chadi, a kotun duniya

Hissene Habre
Image caption Shekaru takwas yana mulkin Chadi

Kotun duniya da ke Hague ta fara sauraron kara a kan tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, wanda ake zargi da aikata mugayen laifuka a kan bil'adama.

Kasar Belgium na son a tasa keyar Hissene Habre din zuwa birnin Hague daga Senegal inda yake zaman gudun hijira tun bayan da aka hambarar da shi, shekaru talatin da biyu da suka gabata.

A cewar lauyoyin kasar ta Belgium, hukumomin Senegal basu yi wani yunkuri ba na bincikar Hissene Habren, ko kuma tuhumarsa.

Ana zarginsa ne da hannu wajen kuntata wa mutane dubu arba'in lokacin mulkinsa na shekaru takwas.

Tsohon shugaban kasar Chadin ya jima yana gudun hijira a kasar Senegal tun lokacin da aka tumbuke shi daga kujerar muliki a shekarar 1990.

Kasar Belgium ta yi kira ga kasar Senegal da ta maido da shi.

Zuwa yanzu dai Senegal ta ki ta amince.

Dalilin da ya sa ke nan Belgium ta kai matsalar a gaban kotun hukunta manya laifuka ta duniya da ke birnin Hague.