An zargi Syria da kisan gilla a Homs

Barna a birnin Homs Hakkin mallakar hoto q
Image caption An ga hotunan gawawwakin yara cikin jini

Masu fafutika a Syria sun zargi gwamnatin kasar da karkashe mata da kananan yara a birnin Homs.

Wasu hotunan bidiyo, wadanda ba a iya tabbatarwa ba, sun nuna wasu gagawakin mutane da aka yanka.

Hotunan sun hada da na kananan yara, cikin jini.

Ga alama kuma wasu daga cikin samarin da aka kashe suna da raunukan harbin bindiga a goshinsu.

Gidan talabijin gwamnatin kasar ta Syria ya amsa cewa an gano gawakin, amma ya dora alhakin kisan mutanen a kan wadanda ya kira kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague, ya fada wa awni taron ministocin harkokin waje a Hedkwatar Majalisar Duniya, cewa lokaci ya yi na nuna shugabanci da hadin kai wajen samar da hanyar warware rikicin Syria.

Ya ce kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya gaza, kuma ya kamata ya yi aiki da muriya guda dangane da batun na Syria.

Ya ce, abin karfafa gwiwa yadda kowa ke magana a kan hanyar warware rikicin ta fuskar siyasa ko yadda za a kai agaji ga mutanen da rikicin ya ritsa da su, amma abun da ya rage shi ne wadannan kasashe su zartar da wani kuduri a kan batun na Syria.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce kasaras na nuna matukar damuwa dangane da halin da ake ciki a Syriar.

ta kuwa Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, kira ta yi ga Rashar da China da su goyi bayan shirin Kungiyar Kasashen Larabawa na warware rikicin siyasar kasar ta Syria.

Karin bayani