Ivory Coast ta samu sabuwar Gwamnati

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, yayinda ake rantsardashi

Kasar Ivory Coast za ta samu sabuwar gwamnati a yau, bayan sauka daga kan karagar mulki da Fira Minista Guillaume Soro yayi ranar Alhamis da ta gabata.

Saukar da gwamnatin da kuma Fira Ministan sukayi na nuni da sauyawar mulki a kasar.

Tsohon madugun yan tawaye Soro an zabe shi a jiya a matsayin shugaban majalisar kasar abunda ya sanya ya zama na biyu ga shugaban kasar.

Wannan na nuni da alamun sabuwar daukakar mulki ga dan siyasar wanda ya shekaru goma baya; shugaban dalibai ne da yayi anniyar juyin mulki sanna kuma ya shafe shekaru biyar yana jagorancin Gwamnatin Kasar Ivory Coast.

Matakan siyasar da Guillaume Soro ya hau kamar littafi ne mai shafuka da dama.

Sai dai Kakakin daya daga cikin Jamiyyun adawa wanda suka mika wuya ga tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo, Danielle Boni Clavier, ya koka cewa nada Mr Soro ya sabawa kundin tsarin mulkin kaasar saboda acewarsa bai kai shekaru mafi karanci da ake bukata ba wato shekaru arbain.Shaura watannin biyu.

Tunda Giyom ya samu shekaru biyar a matsayin shugaban majalisar kasar, akwai tantama kadan ko idanunsa nan gaba zasu sake hararar kujerar shugabancin kasar.

Amma fa neman shugabancinsa na bukatar ya gamsar da yan Ivory coast da dama wanda suke kallonsa a matsayin mutumin da ya jagoranci yan tawaye a 2002.

Karin bayani