An kashe 'yan sanda biyu a Gwammaja a Kano

boko haram
Image caption Wasu 'yan Boko Haram da aka kashe

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wayeba sun kai hari ga jami'an tsaro a wajen binciken abubuwan hawa a unguwar Gwammaja dake tsakiyar birinin.

An kai harin dai dazu da yamma, inda wasu da suka ga abinda ya faru suka ce an kashe 'yan sanda biyu da soja daya, tare da jiwa wani farar hula daya rauni a kafa sakamokon harbin da aka yi masa.

Rundunar samar da tsaro a jihar Kano tace ta tabbatar da lamarin inda tace daya ta kashe daya daga cikin maharan.

A 'yan makwannin jihar Kano na fuskantar kalubalen tsaro wadanda wasu daga cikin 'yan Boko Haram suka amsa cewar sune suka kaddamar da hare hare.