Zaman dar dar a arewacin Najeriya

Harin bom a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin bom a Najeriya

Al'umar garin Mubi na jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya na zaman dar-dar, bayan wani dauki-ba-dadin da jami'an tsaro suka yi da wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba.

Mazauna garin dai sun ce tun cikin dare suka ji amon fashewar abubuwa da kuma karar harbe-harben bindiga.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar a kalla mutane biyar.

A jiya mutum shida ne suka rasa rayukansu, a wani kisan-gillar da mazauna garin suka zargi jami'an tsaro da yi, zargin da jami'an tsaron ba su ce fayyace matsayinsu a kai ba

A Jihar Filato kuma, mutane kimanin ashirin ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, a tashin bam da kuma tashe-tashen hankula da suka biyo bayan harin da aka kaiwa wata majami'a a Jos, a ranar Lahadi.

A yau ma an wayi gari da zaman dar-dar a birnin, inda wuraren kasuwanci suka kasance a rufe, yayin da daliban jami'ar Jos suka toshe babbar hanyar zuwa jihohin Bauchi da Gombe.

Daliban su na nuna rashin jin dadinsu game da jikkata wasu daga cikin dalibai a tashin hankalin da aka yi a jiya.

Daga baya hukumomin tsaro sun sake bude hanyar.

Karin bayani