An kashe mutane 15 a Pakistan

pakistan Hakkin mallakar hoto v
Image caption Wadanda suka mutu a Pakistan sakamakon hari

Jami'an tsaro a Pakistan sunce an kashe wasu mutane goma sha da ake zargin yan gwagwarmaya ne a wasu hare hare da makamai masu linzami guda biyu daban daban da wani jirgin Amurka marar matuki ya kai.

Hare haren sun hari yan gwagwarmayar ne a yankin kabilu na Kudancin Waziristan, a kan iyaka da Afghanistan.

Rahotanni sunce daga cikin wadanda aka kashe har da manyan kwamandoji 2 a wani bangaren yan gwagwarmaya mai fada aji.

Karin bayani