BBC navigation

Amurka ta yi marhabin da hukuncin da aka yanke wa Lubanga

An sabunta: 14 ga Maris, 2012 - An wallafa a 19:10 GMT
lubanga

Thomas Lubanga

Amurka ta yi marhabin da samun jagoran sojin sa kan Congo, Thomas Lubanga, da laifin aikata laifukan yaki, tana mai bayyana hakan a matsayin wani mataki na tarihi kuma mai muhimmanci wajen yin adalci ga jama'ar Congo.

Kotun manyan laifuka ta duniya dake a Hague -- wadda Amurka ba ta amince da ita a hukumance ba -- ta samu Thomas Lubanga da laifi nadauka da kuma yin amfani da yara kanana a matsayin soji.

Da yake karanta hukuncin alkalin da ya jagoranci zaman, Adrian Fulford ya ce a fili take Kungiyar Mr Lubanga ta yi amfani da yara a matsayin soji.

Ya ce "kotu ta gamsu ba tare da wata tantama ba cewar kungiyar UPC/FPLC ta yi amfani da yara yan kasa da shekaru 15 domin shiga cikin rikice rikice gadan gadan, hade da lokuttan yake yake".

Wannan ne dai karo na farko da kotun ta samu wani da laifi tun lokacin da aka kafa ta shekaru 10 da suka wuce.

An aikata laifukan ne kuma tun kusan shekaru 10 da suka wuce, a lokacin wani mummunan rikicin kabilancin da ya barke a arewa maso gabacin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

A wani zama nan gaba za a bayyana hukuncin da Mr Lubanga zai fuskanta.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.