Human Rights tayi kira akai Syria ICC

Hakkin mallakar hoto internet
Image caption Phil Robertson, Matamakin Daraktan Human rights watch, a yankin Asia

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tayi kira da a gurfanarda wadanda suke da hannu akan azabtarda farar hula a Syria lokacin da ake zanga zangar kin jinin gwamnatin.

Amnesty tace Dakarun soji na shugaba Assad sun kirkiri wata hanyar azabtarwa don cin zarafi da tsoratar da wadanda suka shiga hannunsu.

Kungiyar dai ta ce ta kidaya azabtarwa kala daban daban har guda talatin da daya a lokacin da take tambayoyi ga yan Syrian da suka tsere zuwa Jordan.

Haka kuma tayi kira ga Kotun aikata laifuffuka ta ICC da ta buncika azabtarwar ko da yake tace siyasa tayiwa ICC dabai-bayi, saboda kujerar naki da Kasashen Rasha da China sukaita nanata hawa a Kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai tayi kira ga Hukumar dake kula da kare hakkin Dan Adam a Majalisar Dinkin Duniyar da ta tattara bayanai da ka iya sa ayi gurfanarwar. Haka kuma ta ja kunne ga wadanda ake zargin na cin zarafin; da su kwana da sanin cewa hukunci zai yi aiki a kansu.