BBC navigation

Wata kotu ta sami Lubanga da laifi

An sabunta: 14 ga Maris, 2012 - An wallafa a 08:02 GMT

shugaban Kasar Congo, Joseph Kabila

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a Hague ta kama shugaban mayakan sa kai a Jamhuriyar Demokradiyar Congo Thomas Lubanga da aikata muggan laifuka a lokacin yaki kuma wanan shine hukuncin farko da kotun zata yanke tun kafuwarta shekaru goma da suka wuce.

An dai kama Mr Lubanga da laifin amfani da yara masu shekaru kasa da goma sha biyar a matsayin soji.

Laifukan sun auku ne kusan shekaru goma da suka wuce a lokacin da rikicikin kabilanci ya barke a Arewa maso gabashin jamhuriyar Demokradiyar Congo.

Sai dai a nan gaba ne zaa yankewa Thomas Lubanga hukunci.

A shekerar 2005 ne kotun manyan laifuka ta gabatarda sammacin farko kan shugaban 'yan tawayen Uganda, Joseph Kony.

Ana zargin kungiyarsa ta lord resistance Army da aiwatar da muggan laifuka a kasashe da dama a tsakiyar nahiyar Afrika kuma kawo yanzu ba'a san wurin da yake ba

A

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.