Hukumar SSS ta nuna mutane 8 akan kashe turawa

mac manus Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Chris McManus na Birtaniya

A Najeriya hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS tace, mutumin da ake zargi da kitsa kamewa da kuma kashe muntane biyu 'yan kasashen Birtaniya da Italiya cikin makon jiya a Sokoto ya mutu yayin da jami'an tsaro ke kokarin kama shi.

Hukumar tsaron ta SSS ta kuma nunawa manema labaru mutanen da ake zargi da hannu a kamawa da kuma kisan 'yan kasashen wajen biyu.

Kisan mutanen biyu dai a Sokoto ya haddasa kalamai masu zafi tsakanin Birtaniya da Italiya.

Dan Birtaniya Chris McManus da Franco Lamolinara sune mutanen biyu da suka gamu da ajalinsu.

Mutane takwas ne aka nuna a bainar jama'a a matsayin wadanda ke da hannu a lamarin.

Karin bayani