An kashe mutane biyar a birnin Mogadishu

hari a Somalia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hari a Somalia

Mutane akalla biyar aka kashe a wani harin kunar bakin wake da bam a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Lamarin ya auku ne a kofar fadar shugaban kasa, yankin da aka tsaurara matakan tsaro a cikinsa.

'Yan gwagwarmayar Islama na kungiyar Al-Shabab sun ce su ne suka kai harin.

Kungiyar ta kai hare hare nan da can, a birnin na Mogadishu tun daga lokacin da aka fatattake ta daga birnin a bara.

Wakiliyar BBC ta ce Mogadishu babban birnin na Somalia na karkashin ikon dakarun kungiyar tarayyar Afrika su dubu sha biyu, dake aiki tare da dakarun Somalia, ana jin cewar suna samun nasarar korar Al Shabaab daga yankunan da suke da karfi.

Sai dai wannan hari na baya bayan nan zai kasance wani koma baya ga samun tabbatar da tsaro a birnin.