Santorum, ya samu nasarar zabe,

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kasar Amurka Barrack Obama

Tsohon Sanata daga Pensylvania, Rick Santorum, ya samu nasarar zaben fitar da gwani a Jihohin Mississippi da Alabama, don neman zama dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar Republican a kasar Amurka.

Masu nazarin Al'amurra dai na cewa nasarar da Mr Santorum ya samu a Kudanci, zai kara karfafa matsayinsa na zama wanda zai iya yiwuwa ya yiwa jam'iyyar Republican takara a madadin Mitt Romney, wanda ada shi yake kan gaba.

Mr Santorum ya Samu nasara ne a Alabama inda yadoke Newt Gingrich ya zama na biyu shi kuwa wanda yake kan gaba Mitt Romney ya zama na uku.

A yan mintoci kadan baya kuma gidajen Talabijin suka sake bada sanarwar cewa ya samu nasara a Mississippi, ko da yake dai a wannan karon ya samu nasarar ne da tazara kadan.

Yankin Kudancin wanda ke da rinjayen masu kishin addinin Kiristanci kusan ko yaushe zai iya zama garin da Mr Santorum mai raayin rikau zai samu goyon baya sosai.

Wannan ya bawa bangaren Santorum kwarin gwiwar ci gaba da yakin neman zaben don kada Mitt Romney, amma fa tsohon gwamnan Massachusetts har yanzu na kan gaba a bangaren wakilan da ake bukata don cin zaben futarda gwanin.

A gwari gwari dai zai zama abu mai dan karen wahala ga wani ya kamoshi. Newt Gingrich dai bai karaya ba , Sai dai yadda alamurra ke tafiya yanayin baya ne a karawar.

Abunda yake a zahiri dai ga dukkan yan takarar shine kowanne dai na da sauran tafiya a kokarin samun nasarar zaben gaba daya.

Karin bayani