Bankin Islama zai taimaka wa karatun almajirai

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ilmin boko zai amfani almajirai

Bankin raya kasashe na Musulunci na Duniya, zai bai wa Najeriya bashin dala milyan casa'in da biyar, wadanda za a yi amfani dasu don hade tsarin karatun tsangaya da kuma tsarin ilimin boko a kasar.

Shugaban bankin musulucin na duniya Dr Ahmad Muhammad Ali, ya shaida wa manema labaru a Abuja cewa ana sanya ran hakan zai taimaka wajen takaita matsalar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, kungiyar dake adawa da tsarin ilimin boko.

A nata bangaren gwamnatin Najeriyar ta ce za a yi amfani da kudaden wajen taimakawa jihohin da iyaye ke tura 'ya'yansu zuwa makarantun allo na tsangaya.

Ana dai ganin samar da makarantun da za a hada koyon karatun Islama da na boko, zai taimaka wajen samar da suka iya hagu suka kuma iya dama, abin da zai kara amfani ga karatun nasu.