Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Boko Haram

Boko Haram
Image caption Boko Haram ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce a cikin makon jiya ne, gwamnatin kasar ta yi tattaunawar farko a fakaice da 'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, a wani yunkuri na cimma tsaigaita bude wuta tsakanin bangaroin biyu.

Lamarin ya fara fitowa ne a lokacin da wata jarida a Najeriya ta wallafa cewa Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad ta zabi wani shahararren malamin addinin Musulunci a matsayin wanda zai fara tattaunawa ta farko a madadinsu domin kawo karshen hare-haren da suke kaiwa.

Rahotannin sun bayyana cewa kungiyar ta bada wasu sharudda da suka hada da sako dukkan 'yayansu da ake tsare da su, sannan a basu tabbacin cewa za a tsare lafiyarsu idan suka fito fili suka bayyana kansu.

Editan BBC a Abuja Bashir Sa'ad Abdullahi, ya ce majiyoyi da dama sun tabbatar masa da cewa akwai wannan maganar.

"Sai dai sun nuna cewa a yanzu ana mataki na farko ne, ba a fara tattaunawar gadan-gadan ba".

Kungiyar ta kai hare-hare da dama

Kuma ma wadanda suke gudanar da tattaunawar ba sa so maganar ta fito, haka-zalika wadanda ke cikin tattaunawar ba sa son su yi magana a yanzu don kada su kawo tarnaki ga yunkurin tattaunawar.

Kawo yanzu dai kungiyar ta Boko Haram ba ta ce uffan ba, haka ita ma kuma gwamnatin ta Najeriya.

Sai dai a baya jami'an gwamnatin ta Najeriya sun nuna cewa a shirye suke su tattauna da 'ya'yan kungiyar domin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su.

Ita dai Boko Haram na kokarin kafa gwamnatin Islama ne a wasu jihohin kasar ta hanyar fada da jami'an tsaro, sai dai da dama daga cikin 'yan Najeriya ba sa goyon bayan yadda kungiyar ke kai hare-hare.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu samakon hare-haren da kungiyar take kaiwa a sassan kasar daban-daban.

Karin bayani