Amurka ta ce ta kuduri aniyar ci gaba da tattaunawa da Taleban

taliban Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Taliban

Amurka ta ce za ta ci gaba da kokarin ganin an sasanta tsakanin bangorori a Afghanistan, duk da cewa kungiyar Taliban ta ce ta dakatar da tattaunawar kawo zaman lafiya da ake san farawa.

Wani mai magana da yawun Shugaba Obama ya ce ba za a kawo karshen rikicin da ake yi a Afghanistan ba matsawar ba a cimma wata yarjejeniya ta siyasa ba.

Kungiyar Taliban tana ta tattaunawa ne da Amurkawa a kan bude ofishinta na siyasa a Qatar da kuma batun sakin wani sojin Amurka da aka sace, a matsayin musayarsa da mayakan Taliban biyar.

Majiyoyin Amurka sun ce Washington na san sa gwamnatin Afghanistan a cikin sasantawar, amma kungiyar Taliban ta ki saboda tana daukar gwamnatin Hamid Karzai a matsayin haramtacciya.

Wasu majiyoyi a Amurka sun ce Amurkawan na san gwamnatin Afhanistan ta shiga tattaunawar - abida Taliban ta ki yadda saboda tana daukar gwamnatin Shugaba Hamid Karzai a matsayin haramtacciya.

A karkashin yarjejeniyar musayar fursunonin, za'a saki mayakan Taliban su biyar inda su kuma za su saki wani sojan Amurka daya da aka sace.

Kungiyar ta 'yan Taliban dai ta ce ta dauki matakin dakatar da tattaunawar ce da Amurka a kan batun kafa wani Ofishin ta na siyasa a Qatar da kuma musayar fursunoni saboda sharuddan da Amurkar ta gindaya ma su, wadanda suka ce ba za ta laminta da su ba.

Wasu majiyoyin Diplomasiyyar Amurka sun ce gwamnatin Amurkar ta fadawa 'yan Taliban din cewa dole ne jami'an gwamnatin Afghanistan su halarci duk wata tattaunawar da zaa yi.

Sai dai bisa dukkan alamu, 'yan Taliban din sun ce ba za su yarda da hakan ba, saboda suna daukan gwamnatin shugaban Hamid Karzai, a matsayin wata haramtacciyar gwamnati.

A kan batun musayar fursunonin kuwa, an yi imanin cewa nan da 'yan makonni ne aka shirya zaa yi musayar wasu mayakan Taliban 5 da ake tsare da su a sansanin Guantanamo Bay a kan wani sojin Amurka da 'yan Taliban din suka sace.

Wannan dai wani babban koma baya ne ga yunkurin da ake yi na kaddamar da shawarwarin zamann lafiya da mayakan na Taliban.

A halin da ake ciki kuma, shugaban Hamid Karzai, ya bukaci Sakataren tsaron Amurka, Leon Panetta da ya bada umarnin mayar da duka sojojin kawance zuwa sansanoninsu dake Afghnaistan, abun da zai kawo karshen sintirin da suke yi a kauyuka da garuruwan kasar.

Ya ce sojojin Afghanistan suna da karfin da za su tafiyar da harkokin tsaro a wadannan wurare.

Har yanzu dai sojojin kawancen ba su dakatar da sintirin nasu ba, kuma da ma an shirya za su koma sansanonin nasu nan da karshen shekara ta 2013.

Karin bayani