'Dan Majalisa ya nemi cin hanci-Oteh

arunma oteh Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabar hukumar SEC Arunma Oteh

Shugabannin majalisar wakilan Najeriya na can suna ganawa, bayan an zargi dayansu da aikata laifin neman cin hanci.

A jiya ne shugabar hukumar dake kula da kasuwannin hannayen jari ta kasar, Mis Aruma Oteh, ta ce, shugaban kwamitin majalisar dake sa ido akan kasuwannin hannayen jari, Honourabue Herman Hembe, ya nemi cin hanci na kimanin naira miliyan arba'in da hudu daga gare ta.

Ta ce bai kamata ya cigaba da rike mukamin nasa ba, to sai dai dan majalisar ya musanta zargin.

Lamarin dai ya auku ne jiya yayin da kwamitin majalisar ke zaman bincike matsalolin da suka dabibaye kasuwannin hannayen jari a Najeriya.

Koda baya dai an sha zargin 'yan majalisar dokokin Najeriyar da neman cin hanci domin daga wasu ma'aikatun gwamnati da suke kula da ayukansu.