Majalisar Dinkin Duniya zata bada Agaji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption yan Syria na tserewa daga Idlib

Majalisar Dinkin Duniya zata aika da jami'anta da zasu shiga ayyukan agaji wanda gwamnatin Syria ke jagoranta a karshen wannan makon mai zuwa.

Ayyukan agajin dai, zai kuma bada damar duba halinda mazauna yankunan da rikicin yafi kamari suke ciki, wadanda suka hada da biranen Homs dana Deraa da kuma Hama.

Piraminsitan Kasar Lebanon Najib Mikati ya kuma musanta cewa dangantakarsa da Damascus ta hana gwamnatinsa tallafawa 'yan gudun hijirar da suka fito daga Syria.

Mr Mikati ya shaidawa BBc cewa an taimakawa yan gudun hijirar da wajan kwana da magunguna kuma an tarbesu ba kuma wanda aka kora zuwa Syria.

Ya dai tabbatar da matsayin kasarsa cewa sunyi Allah wadai da abunda yake faruwa a Syria; amma fa yace ta bangaren agaji suna yin aiyukansu babu amaja. Sun bada wajan kwana da magunguna harma da samarda makarantu ga wadanda suka tsere zuwa Kasar Lebanon.

Shi kuwa Sirikin Shugaban Kasar Syria, Bashar Al Assad, ya kwatanta rikicin Syriyan ne da tarzomar da akayi a London shekarar da ta gabata.

Yayinda yake magana da Jaridar Telegraph, fawaz Akhras ya kare amfani da karfin soji da sirikin nasa yayi akan masu zanga zangar kyamar gwamnatin Syria. Yace shugaba Assad yana da hakki ya kare tsaron alummarsa.

Mazauna yankunan da akayi ta artabu a Syrian na cikin wani mawuyaci hali.