An bayyana sunan sojan da ya kashe mutane 16

sergeant Robert Bales Hakkin mallakar hoto DVIDS
Image caption sergeant Robert Bales

An bayyana sunan sojin Amurkan nan wanda ake zargi da halaka mutane goma sha shidda yan wani kauye a kasar Afghanistan.

Sunansa dai shine sergeant Robert Bales.

A halin yanzu dai an garzaya da shi Amurka inda za a tsare shi a sansanin soji na Kansas.

Lauyan dake kare shi ya bayyana shi a matsayin kwararren soja, kuma uba mai kaunar 'ya'yansa, wanda ya samu rauni a kwakwalwarsa lokacin da yake a Iraqi.

To sai dai mahukunta sun ce Sergeant Bales yayi ta shan barasa a daren da ya yi wadannan kashe-kashe.

A ranar Jumuar da ta gabata ne shugaba Karzai na Afghanistan ya ziyarci mutanen kauyen, da yan uwan wadanda sojan ya kashe, inda ya ce mutanen da ya gana da su, sun ba shi labarin da ya sha banban da abinda Amurka ke cewa game da kashe kashen. Ya ce akwai alamun cewa ba soja guda ne ya yi wannan aika aika ba.

Karin bayani

Labaran BBC