An samu cikas a tattaunawar gwamnati da Boko Haram

Kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Boko Haram

A Najeriya, shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci ya ce sun janye daga tattaunawar sulhu da suka fara gudanarwa da jami'an gwamnatin kasar da kuma 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlis Sunnati Lidda Awati wal Jihad, da aka fi sani da Boko Haram.

A wata sanarwa daya fitar, shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci Dr. Ibrahim Datti Ahmad ya ce shi da sakataren majalisar sun yanke shawarar janyewa daga tattaunawar ce saboda sun ga alamun cewa jami'an gwamnatin kasar bada gaske suke ba a tattaunawar da aka fara yi da shugabannin kungiyar Boko Haram.

Sanar war ta ce taga alamun babu sirri game da abubuwan da suka fara tattaunawa akai tatre da jami'in dake wakiltar gwamnatin a tattaunawar.

Abinda ya sa suke da shkkun kan ko ma dama gwamnatin da gaske ta ke wajen ganin an sasanta da 'ya 'yan kungiyar ta Boko Haram, wadanda a yawancin lokuta ke daukar alhakin kai wasu hare hare a kasar.

Karin bayani