Ana neman a agazawa hukumar Falasdinawa

Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF

Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, ya yi kira ga kaashen da ke ba da bashi da su cika alkawarin da suka yi na taimaka wa Hukumar Falasdinawa.

A cikin wata wasikar tuni da aka gabatar gabanin taron kasashen da ke ba da bashin da za'a yi a birnin Brussels a makon gobe, IMF ya ce dala milyan dari biyu ne aka alkawarta ma Hukumar Falasdinawan a bara don gudanar da ayyukan jama'a, amma har yanzu ba a ga ko centi guda ba.

Wadda ta fi ba da agajin, wato Amurka, a bara ne ta dakar da ba da agajin bayan da Shugaba Mahmoud Abbas ya bijire wa Amurkar, ya kuma yi shelar neman kafa kasar Falasdinawa a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya.