An kama tarin nakiyoyi a Afghanistan

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai

Jami'an tsaro a Afghanistan sun ce sun kama tarin nakiyoyi a sassa daban-daban na kasar.

Wakilin BBC ya ce, wani kakakin Hukumar tsaro ta kasar ya sheda wa taron manema labarai a Kabul cewa, an kama tarin nakiyoyin ne a kusa da gidan gwamna a birnin Mazare Sharif da ke arewacin kasar.

Kamar ton biyu da rabi ne aka samu a kusa da gidan gwamnan.

An kama mutane shidda da jami'an suka ce wadanda ake zargin sun shirya kai hari ne ranar Talata, ranar bukin sabuwar shekarar Farisawa, kuma gano nakiyoyin ya yi maganin mummunan zubar da jini.

Karin bayani