An kammala zaben shugaban kasar Guinea Bissau

Zben Shugaban kasa a kasar Guinea Bissau Hakkin mallakar hoto d
Image caption Zben Shugaban kasa a kasar Guinea Bissau

A yanzu haka an fara tattara sakamakon zaben shugaban kasa a kasar Guinea Bissau da aka gudanar a yau dinan.

An dai gudanar da zaben ne bayan, bayan rasuwar marigayi Malam Bacai Sanha, sakamakon rashin lafiyar da yai fama da ita.

'Yan takara tara ne ke fafatawa a zaben, ciki har da tsohon shugaban kasar, Kumba Yalla, wanda sojoji suka hambarar daga mulki a can baya da kuma tsohon Firaminista Carlos Gomes Junior.

Tun fitowar rana jama'a suka fara fitowa suna kafa layi domin kada kuri'arsu.

An dai gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Karin bayani