Hukumomin Libya sun bukaci a mika masu al Sanussi

Abdallah al-Sanussi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abdallah al-Sanussi

Gwamnatin kasar Libya ta nemi a mika ma ta Abdullah al Sanussi, tsohon shugaban hukumar leken asiri kuma na hannun daman marigayi Kanar Mu'ammar Ghaddafi wanda aka kame a Mauritania.

Hukumomin Mauritania sun ce an kama shi ne a filin saukar jiragen sama na Noukchott bayan ya isa can daga Morocco ta hanyar amfani da fasgo na jabu, duk da yake dai har yanzu babu wata shaidar da aka buga ta kame shi.

Birtaniya ta jinjinawa hukumomin kasar Mauritania bisa kama Abdullah al Sanussi.

Gwamnatin kasar Faransa kuma ta bayyana yiwuwar bukatar a mika mata Mr Sanussi, bisa zarginsa da hannu wurin tada bam a jirgin saman Faransa a shekarar 1989.

Karin bayani

Labaran BBC