Fasfo din diplomasiyya mu ka ba Bashir: Inji Bazoum

Bazoum Muhammed, ministan harkokin wajen Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bazoum Muhammed, ministan harkokin wajen Nijar

A jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da soke Fasfo din da suka ba tsohon darektan fadar marigayi Kadafi, Bashir Saley Bashir, kamar yaddaya nema.

Wannan dai ya biyo bayan irin ce-ce-ku-cen da ake ta yi game da bashi Fasfo din a ciki da wajen kasar ta Nijar.

A yau ne ministan harkokin wajen Nijar din Bazoum Mohamed ya tabbatar da haka a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Yamai.

Malam Bazoum Mohamed ya ce bada Fasfo din diplomasiya na Nijar ga tsohon darektan fadar Kadafi bai saba ma doka ba, haka zalika ba sabon abu ba ne don kuwa gwamnatocin da suka gabata sun sha yin haka a can baya.

Karin bayani