BBC navigation

An fara yunkurin ceto 'yan Pansho a Najeriya

An sabunta: 19 ga Maris, 2012 - An wallafa a 16:26 GMT
Shugaban hukumar EFCC

Shugaban hukumar EFCC

A Najeriyar, hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa wato EFCC ta tabbatar da cewa tana binciken wasu direktoci bakwai da skuma wani babban sakatare a ma'aikatun gwamnatin tarayya bisa zargin sama da fadi da kudaden fansho kimanin naira biliyan biyu.

Hakan dai na zuwa ne 'yan makonni bayan majalisar dattawan Najeriya ta kaddamar da bincike akan badakalar zargin sama da fadi da kudaden da aka ware don biyan fansho.

A binciken da kwamitin ya gudanar ya gano a baya duk wata an yi sama da fadi da kimanin naira biliyan daya na kudin fansho din ma'aikata a ofishin 'yan sanda na kasar , kana akwai wasu makudan kudadan da aka boye ana cin kudin ruwansu, baya ga cek-cek da ake rubutawa na bogi ana fitar da kudaden.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.