Za a bude taron cinikayya tsakanin China da ECOWAS

kasuwancin China da ECOWAS Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption kasuwancin China da ECOWAS

A yau ne za a bude wani babban taro kan harkokin cinikayya tsakanin China da kasashen kungiyar Ecowas ta yammacin Afrika.

Taron wanda za a yi a kasar Ghana, ministotin cinikayya da manyan jami'an gwamnatoci da kuma 'yan kasuwa daga bangarorin biyu ne za su harlata.

China dai ta shiga harkokin kasuwanci a nahiyar Afirka kain da nain, inda ta zarta duk wata kasa a duniya.

Wasu kayyakin da Chinan ke shiga da su nahiyar Afirka dai na da saukin kudi, to saidai wasu na zargin cewa ba su da karko.