An yi girgizar kasa a Mexico

Girgizar kasa a Mexico Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Girgizar kasa a Mexico

An samu girgizar kasa a yawancin yankin kudancin kasar Mexico.

Hukumomin binciken abubuwan karkashin kasa na Amurka sun ce ma'aunin karfin girgizar kasar ya kai maki fiye da bakwai da rabi, kuma ya fi karfi ne a kusa da Acapulco dake gabar tekun Pacific.

Kawo yanzu dai babu rahoton irin hasarar da aka tafka.

Sai dai kuma har a babban birnin kasar wato Mexico city wanda keda tazarar sosai daga wajen an dan ji girgizar.

Gine gine a wajen sun girgiza sannan mutane sun fito kan tituna bisa fargaba.

Kawo yanzu babu wani karin bayani akan lamarin.

Karin bayani