An kai karin hare hare a jihar Kano

matsalar tsaro a Nijeriya
Image caption matsalar tsaro a Nijeriya

Rahotannin daga Kano a arewacin Nigeriya na cewa wasu 'yan bindiga da kawo yanzu ba a tatance ko su waye ba, sun kai wasu hare hare a garin Tudun Wada, dake karamar hukumar ta Tudun Wada a jiya da dare.

An kai hare haren ne a gidan babban jami'in 'yan sanda na yankin, da ofishin 'yan sanda da kuma wani banki wadanda ke kusa.

Mazauna yankin sun ce an lalata ofishin 'yan sandan baki dayansa, inda kuma aka yi barna a gidan jami'in 'yan sandan da kuma bankin.

Daga bisani rundunar sojan Najeriya a Kano sun fidda sanarwa inda suka ce sun kashe tara daga cikin maharan, kuma sun kama mutum biyu da ran su.

Karin bayani