Zaa Tuso keyar Al Sunussi, Inji Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hoton Al Sunussi

Gwamnatin Libya tace Kasar Murtaniya zata tuso keyar dan kasarta shugaban Hukumar Leken Asiri na gwamnatin Ghaddamafi zuwa Libya don fuskantar sharia.

Sai dai wani rahoto daga gwamnatin Murtaniya yace har yanzu basu kai ga yanke hukunci kan abunda zasu yi da Abdullah Alsunussi ba.

Wannan kalamai guda biyu na nuni da rudani da ya ke futowa kan batun tuso keyar abdullah Al Sunussi zuwa kasar Libya.

Kasar Libyan dai ta jima tana nanata neman a tuso keyar dan kasar nata don fsukantar tuhume tuhume a da suka sahfi na kisa da kuma cin zarafin Dan Adam

Mataimakin Fira Ministan Kasar Libyan Mustapha Abu Shagour, shine ya sanar da wannan labari a shafin sa na Twitter, bayan wata ganawa tare da shugaban Mauritanian.

Sai dai hukumomin Mauritanian sun ce ba a yanke shawarar tuso keyar Al Sanusi'n ba, yayin ganawar.

Sai dai Al Sunussin akwai yiwuwar a turashi zuwa kotun laifuffuka ta kasa da kasa dake Hague don fuskantar tuhume tuhume da suke da alaka da murkushe masu bore da sukayi zanga zangar hambare gwamnatin Muahmmar Ghaddafi shekarar da ta gabata.

Karin bayani