Soja sun yiwa fadar shugaban Mali kawanya

mali
Image caption Shugaban Mali Amadou Toumai Toure

Dakaru a tsakiyar Bamako babban birnin kasar Mali sun karbe ikon gidan talabijin na kasar, inda suka hana watsa shirye shirye.

An ji harbe-harbe a cikin birnin a yayinda motoci masu sulke suka zagaye fadar shugaban kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin tsaron kasar ya tabbatar da cewar sojojin suna zanga zanga akan rashin isassun makamai a yakin da suke yi tsakaninsu da 'yan tawayen arewacin kasar.

Tun da farko dai, an soma jin harbe harbe ne a barikokin sojoji dake arewacin kasar a lokacin da ministan tsaron kasar ya kai musu ziyara.

Karin bayani