Anyi wata Girgizar Kasa a Mexico

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption baraguzai a mexico inda akayi girgizar kasa

Wata gigizar kasa mai karfin maki bakwai da digo hudu ta afku a Kudu maso Yammacin Mexico inda tafi kamari a Jihar Guerrero kusa da Acapulco a gabar Pacific.

Gine gine dai sun girgiza, maaiakata da kuma mazauna yankunan a manyan biranen sun fantsama kan tituna cikin dimuwa.

Sai dai zuwa yanzu babu rahoto kan wadanda suka mutu. Hukumomi a garin na cewa gidaje kusan dari takwas sun lalace wasu kuma sun rushe.

wajen da girgizar kasar tafi kamari kusa da Acapulco babu wayar sadarwa. Girgizar kasar dai na daga cikin wadda tafi muni a Mexico tun wadda akayi a 1985, wanda dubban mutane suka rasu.

har izuwa yanzu dai babu babu cikakken bayanai kan asarar rayuka da ma barnar da girgizar kasar ta haifar.

Daraktan Hukumar kiyaye alumma na Jihar, Victor Flores, ya zaiyyanawa masu aiko da rahotanni halin da ake ciki inda yace kusan mahimman abubuwan rayuwa a Jihar Guerrero babu abunda ya samesu. hanyoyi da gadoji da tashar bada wutar lantarki basu lalace ba.

Wannan na nuna cewar duk abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha, da abunci, da hasken wutar lantarki na tafiya yadda ya kamata. Amma illoli dai shine rushewar gine gine.

Karin bayani