Okonjo na cikin 'yan takarar bankin duniya

Ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala da tsohon ministan kudin Colombia Hoze Antonio Ocampo ne 'yan takarar da kasashe masu tasowa ke son a baiwa dayansu shugabancin babban bankin duniya.

Mr. Ocampo ya tabbatar da hakan, kodayake mai magana da yawun Mrs Okonjo-Iweala, Mr. Paul Nwabuikwu yace ba Ngozi ce ke neman mukamin a kashin kanta ba.

Sai dai a wata hira da Okonjo ta ce da BBC lokaci yayi da hukumomin duniya za su bude kofar gogayya da kowa a bisa cancanta.

Amurka wacce ke rike da mukamin bata kaiga tsayar da dan takara ba.

Kasashe masu tasowa na son ganin an samu sauyi kan kwarya-kwaryar yarjejeniyar da aka cimma tun farko wacce ta baiwa Amurka damar rike mukamin babban bankin duniya.

Yayinda nahiyar Turai kuma za ta shugabancin hukumar lamuni ta Duniya kuma