An saki 'yar Burtaniyar da aka sace a kenya

Judith Tebbutt
Image caption Judith Tebbutt

An saki wata 'yar Burtaniya Judith Tebbutt wacce 'yan bindiga suka yi awon gaba da ita a kasar Kenya.

Judith ta shafe watanni shida a hannun wadanda suka yi garkuwa da ita kafin sakinta.

Yanzu haka dai Judith ta isa birnin Nairobi, kuma rahotanni sunce an biya kudin fansa kafin a 'yan Somaliyan da suka yi garkuwa da ita su sake ta.

Babu wanda ya san yawan kudin da aka biya na fansan.

An kama Judith Tebbutt ne a wani wajen shakatawa a Kiwayu dake arewacin Kenya, inda kuma maharan suka kashe mijinta.

A wata hira da akayi da ita bayan sakin na ta, Ms. Tebbutt ta ce wadanda suka yi garkuwa da ita ba su gallaza mata ba, sannan kuma ta zaku ta hadu da danta.