Faransa na son kama dan bindiga da ransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption sojojin Faransa dauke da akwatin gawa

A Kasar Faransa artabu tsakanin jami'an tsaron da suka goge kan harkar yaki da ta'addanci da kuma wanda ake zargi da kisan mutane bakwai ya shiga rana ta biyu.

Anji karar harbe- harbe da fashewar wasu abubuwa a tsakiyar daren jiya a Kudancin birnin Tulouse, inda Mohammed Merah yake a wani gida, wanda tawwagar Jami'an tsaron suka killace.

Sai dai akwai rahoton da yake nuni da cewa dan bindigar, da kuma Jami'an tsaron basa jin duriyar juna.

Ana zargin Muhammed Merah da kashe yara uku da malaminsu da kuma sojoji uku.

Harin ya zo ne a lokacin da za ayi zabe a Kasar mai cike da ada-tsaki na zargin shugaba Nicolas Sarkozy da sakaci kan fargabar masu kada kuri'a da kuma karfafa wariyar launin fata, da fatan jan hankalin masu marawa ra'ayin rikau baya.

Ministan cikin gida na Faransa, claude Guent ya ce yana so a kama wanda ake zargin da kashe- kashen don aji menene abinda ya sa a gaba.

Karin bayani