Dubbai sun yi zanga-zanga a Florida

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption hoton Barrack obama da Matarsa Michelle

Dubban mutane ne suka shiga zanga-zanga a Jihar Florida dake Amurka don neman a tsare wani jami'in sa- kai dake lura da aikata laifuka wanda ya harbe wani saurayi bakar fata.

Gwamnan Florida Rick Scott, ya nada sabon mai gabatarda kara don ya jagoranci bincike kan lamarin.

Kusan wata guda kenan wanda ake zarginsa da kisan George Zimmerman, ba a kamashi ba abinda ke daurewa a'lummar bakaken fata 'yan Amurka dake Sanford kai.

Wannan ya jawo zanga-zanga a Florida inda dubban mutane suka fito suna bukatar a kama Jami'in sakai mai lura da masu aikata laifuffuka wanda ya harbe saurayin bakar fata.

Kisan matashin Trayvon Martin da aka yi kusan sati hudu da suka wuce ya haifar da fushi sosai.

An dai yi kakkausan suka ga babban jami'in 'yan sanda na Sanford, Bill Lee kan rashin kama George Zimmerman, inda yake kare shi cewa yayi hakan ne don kare kansa.

Haka ma dai wani jangwarzo mai fafutuka Al Sharpton yayi ta nanata bukatar a dau mataki mai tsauri, ciki har da kama Mr Zimmerman.