Kasashen duniya sun tir da sojin Mali

Juyin mulki a Mali Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juyin mulki a Mali

Kasashen duniya suna ta yin Allah Waddai da sojojin Mali, wadanda suka hambarar da gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure.

Amurka ta bi sahun Faransa da kungiyar Tarayyar Afruka wajen yin tir da juyin mulkin, tare da yin kiran da a dawo da mulkin Demokradiyya a kasar nan take.

Wani kakakin bijirarrun sojojin, Laftana Amadou Konare, ya ce za su maida mulkin ga farar hula ne kawai, da zarar an tabbatar da cewa an samu hadin kan kasar da kare iyakokinta.

Ya ce, muna sanar cewa mun rufe iyakokin sama da na kasa da kasashen dake makwabtaka da mu, kuma muna kira ga al'ummar Mali da su kwantad da hankalinsu tare da kasancewa a cikin gidajensu.

Masu shari sun ce sojojinsun yi bore ne, bayan da 'yan tawayen Abzinawa suka samu galaba a kan dakarun gwamnati a Arewacin kasar.

Karin bayani