Okonjo na takarar shugabancin bankin duniya

Ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala

Ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta tabbatar da cewa za ta shiga takarar neman shugabancin babban bankin duniya.

Mukamin dai Amurka ce ke rike da shi tun bayan yakin duniya na biyu.

A yau ne wa'adin da aka diba na maye gurbin shugaban babban bankin duniya mai barin gado, Robert Zoellick zai kare.

Ministan kudin Afrika ta Kudu, Pravin Gordon ya bayyana goyon bayansa ga Okonjo na takarar shugabancin babban bankin.

Ya bayyana haka ne a yayinda Ngozi ke tsaye a kusa da shi, a wani taron manema labarai a Pretoria.

Haka ma kasar Angola na goya mata baya.

Sai dai kawo yanzu Amurka ba ta tsayar da dan takararta ba, ga hukumar dake maida hankali kan samar da kudade ga kasashe masu tasowa.

Karin bayani