Martanin MNJ a Nijar kan kama Aghaly Alambo

Aghaly Alambo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aghaly Alambo

A jamhuriyar Nijar tsohuwar kungiyar 'yan tawayen MNJ ta nuna rashin jin dadinta dangane da tsarewar da hukumomin shari'ar kasar ke yi ma shugabanta Malam Agaly Alambo.

Da yake Magana dangane da lamarin Malam Ahmed Waghayyan, daya daga cikin shugabannin tsohuwar kungiyar ta MNJ ya ce ko kadan babu kanshin gaskiya game da zargin da ake yi ma Agaly Alambon .

A ranar Talatar da ta gabata ne dai babban alkali mai kula da al'amurran ta'addanci ya saurari Agaly Alambon dangane da tuhumar da shari'a ke yi masa na cewa yana da hannu a cikin wata badakala da ta shafi safarar makamai da ma hada baki da wasu mutane don aikata ayyukan ta'addanci .

Tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta MNJ ta ce abin takaici ne kama Malam Alambo, kuma ya kamata a guji duk wasu matakai da zasu kawo cikas da shirin zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.

Karin bayani