Nijar ta yi Allah wadai da juyin mulkin Mali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Golpe de Estado en Mali

Gwamnatin Nijar ta bi sahun wasu kasashen duniya da sukayi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Mali.

Gwamantin Nijar ta ce basu amince da juyin mulkin ba, kuma ya sabawa dokokin kasashen kungiyar ECOWAS

Ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar, Bazum Muhammed, wanda juyin mulkin ya rutsa dashi a Mali ya shaidawa BBC cewa juyin mulkin abune da ba zasu lamunta ba.

Sojojin da suka juyawa tsohuwar gwamnatin Kasar baya sun yi juyin mulkin ne kan abunda suka kira gazawar gwamnatin Kasar kan kawo karshen rikicin yan Tawaye Abzinawa dake arewacin Kasar.

Sun ce basu da isassun kayan aikin soja na yakar yan tawayen.

Izuwa yanzu idanun Duniya ya karkata zuwa Kasar ta nahiyar Afrika ta yamma mai makwabtaka da Nijar da Mauritaniya.

Karin bayani