Ana fuskantar bala'i a yankin Sahel - Oxfam

Karancin abinci Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fari na daya daga cikin abubuwan da suka haddasa karancin abinci

Kungiyar ba da agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa farin da ake fama da shi a yankin Sahel na Afrika zai iya zama wani bala'i muddin aka gaza daukar matakin gaggawa na magance shi.

Illolin da fari da hauhawar farashin kayan abinci ke haifarwa sannu a hankali suna kara ta'azzara a yankin yammacin Afrika.

Kungiyar tace kasashen duniya sun yi jinkiri, wajen kai dauki a kusurwar Afrika da Gabashin Afrika a bara, don haka bai kamata hakan ta sake faruwa ba.

Kungiyar ta Oxfam ta kaddamar da asusun neman taimakon gaggawa na fam miliyan ashirin da shidda.

Fadan da aka dade ana gwabzawa tsakanin 'yan tawaye da sojoji a arewacin kasar Mali ya haddasa karuwar matsalar 'yan gudun hijira abinda ke kara nauyin kabulabalen da ya dabaibaye ma'aikata masu bayar da agaji a yankin.

Makwaftan kasashe

Fiye da mutane dubu dari ne fadan ya tilasta ma tserewa daga gidajen su, suna tsallkawa cikin Nijer da sauran wasu kasashen da daama can ke faama da matsalar karancin abincin.

Matsalar dai ba wai a wadannan kasashe ta tsaya ba - har ma da makwaftan kasashe.

"Jama'a da dama kan tsallako daga Nijar zuwa Najeriya domin neman taimakon abinci," a cewar Alhaji Babba Sa'ad Jibia, wani mazaunin kan iyakar Nijeriya da Nijer.

"Bakin su kan fadi karara cewar abinci suke neman taimako ba kudi ba". kamar yadda Bala ya shaida wa BBC.

A kasar Chadi ma...

Kungiyar ba da agajin ta Oxfam ta ce a wasu Kauyuka na sassan kasar Chadi, karancin abincin da ake fama da shi ya tilasta ma mutane gina gidajen Tururuwa suna kwashe hatsin da Tururuwar ta tara.

Darakta mai kula da yankin Afrika ta yamma na kungiyar Oxfam Mamadou Biteye ya bayyana cewar miliyoyin mutane a yankin suna fuskantar wani babban bala'i.

"Dole a tashi tsaye a ba da agaji don hana dubban mutane mutuwa saboda mutanen duniya sun yi biris da halin da suke ciki."

Kungiyar tace irin wannan hali na jinkiri ne a bara ya sa mutane da dama suka mutu a gabashin Afrika sakamakon karancin abincin.

Karin bayani