Ba zamu dade kan mulki ba --Inji Kyaftin Sanogo

Kyaftin Sanogo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kyaftin Sanogo, Sabon Shugaban mulkin sojin Mali

Wanda ya shugabancin juyin mulki a Mali ya shaidawa BBC cewar baida niyyar dadewa a kan mulki.

Kyaftin Amadou Sanogo ya ce zai sauka idan sojojin sun tabbatar da tsaron kasar.

Yayi korafin cewar sojoji basuda makaman da za su iya yaki da 'yan tawayen arewacin kasar.

Kyaftin Sanogo ya ce za a gurfanar da tsaffin shugabanni a kasar gaban tsarin shari'ar kasar.

Kawo yanzu dai babu wanda ya san inda Shugaba Toure yake, kwana biyu bayan da aka yi juyin mulkin.

A halin da ake ciki kuma Kungiyar Tarrayar Turai wato EU ta dakatar da ayyukanta na ci gaba a kasar ta Mali.

Catherine Ashton babbar jami'a a kungiyar ta EU ta bayyana sun yi matukar jin takaici tare da yin Allah wadai da juyin mulki a Mali.

Ta ce suna da tuntuba sosai tare da jama'ar kasar, kuma suna fatar za a maido da doka da oda ba tare da bata lokaci ba.

Karin bayani