Kungiyar Nahiyar Afrika za ta kamo Kony

Image caption Madugun yan tawayen Uganda, Kony

Kungiyar Nahiyar Afrika, tana hada dakaru dubu biyar masu karfi a yankin, don farauto madugun 'yan tawayen Uganda da ya tsere, Joseph Kony.

An kaddamar da kamfe na kamo madugun 'yan tawayen na Lords Resistance Army a shafin yanar gizo a wannan watan.

Jami'in kula da harkokin ta'addanci na yankin ya ce Kony na da zabi uku ne, ko dai ya mika wuya, ko a kamashi, ko kuma tsaka- tsaki

Ita kuwa Majalisar Dinkin Duniya ta yi amannar cewa madugun yan tawayen Mr Kony, yana Afrika ta tsakiya a halin yanzu.

Kungiyar Nahiyar Afrika ta ce Yan tawayen ne sukayi sanadiyyar mutuwar farar hula dubu biyu da dri shida (2,600) tun shekara ta dubu biyu da takwas.

Kony dai ya daina amfani da fasaha ta sadarwa kamar tarho abunda ya sa yayi wahala a kamo shi

Karin bayani